Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daga Salisu Jegus

Ronaldinho

An saki Ronaldinho daga kurkuku an kuma yi masa daurin talala, bayan da aka tsare shi a Paraguay.

Zakaran kyautar Ballon d’Or na 2005 ya yi zaman gidan kurkuku tare da dan uwansa ranar 6 ga watan Maris, inda aka zarge su da amfani da jabun fasfo.

Tun farko an hana bayar da belensu, amma yanzu an amince da biyan fam 648,000 kowanne, sannan za su ci gaba da zama a kasaitaccen otal a birnin Asuncion kafin a gurfanar da su.

Ronaldinho mai shekara 40 da dan uwansa Roberto Assis sun musanta laifin da ake zarginsu.

Lawyansu ya kwatanta garkame su da aka yi da keta doka da cin zarafi.

Alkali Gustavo Amarilla ya ce kudin da aka bayar da su beli ya yi, kuma hakan ne zai tabbatar da ba za su tsere daga kasar ba.

Shi dai Ronaldinho ya ziyarci Paraguay domin tallata littafi da yekuwar tallafawa yara marasa galihu.

Dan wasan wanda ya lashe kofin duniya a 2002 ya taka leda a kungiya da ta hada da Paris St Germain da Barcelona da AC Milan.

A shekarar 2015 dan kwallon ya yi ritaya, bayan da ya kammala wasa a kungiyar Brazil mai suna Fluminense.

Ronaldinho wanda ya lashe kofin duniya a 2002 da Brazil, yana cikin ‘yan kwallon Fifa fitattu 11 na duniya a 2005 da kuma 2006.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *