ZABEN AMURKA 2020
AFRIKA
NAJERIYA
NIJAR
YANKIN HAUSAWA
SHIRYE-SHIRYE
/ Duniya
Zan sake tsayawa takarar shugaban kasa-Trump
Wallafawa ranar: 02/12/2020 – 21:07
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump REUTERS/Carlos Barria
Zubin rubutu:
Abdurrahman Gambo Ahmad
|
Michael Kuduson
Minti 2
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump, wanda ya rasa goyon baya a kokarinsa na kalubalantar nasarar da Joe Biden ya samu a zaben watan Nuwamba, ya fito karara yana bayyana muradinsa na sake tsayawa takarar shugabancin kasar.
A yayin da yake jawabi ga bakin da suka hallarci liyafar Kiristimati da aka shirya a fadar White House, Trump ya bayyana fatar sake ganin su a shekaru 4 masu zuwa.
Duk da cewa ba a bai wa ‘yan jarida damar shiga zauren liyafar da ta samu halartar kusoshin jam’iyyarc Republican da dama ba, bidiyon jawabin shugaban mai barin gado ya samu kai wa ga al’umma.
Kusan wata guda da zaben shugaban kasa a Amurka, har yanzu Trump ya ki amincewa da shan kaye a hannun abokin hamayyarsa na Democrat Joe Biden.
Trump wanda ke ci gaba da gudanar da aikinsa a matsayin shugaban kasa, ya takaita bayyanarsa a bainar jama’a, amma bai kauce wa wallafa sakwannin Twitter , yana mai bayyana fushinsa a kan zargin magudi da yake cewa an yi masa a zaben ba, duk da cewa Atoni Janar dinsa na cewa babu shaidar da ke tabbatar da haka.
A cewar kafar talabijin ta NBC, Trump ya tattauna da mukarrabansa a kan yiwuwar kaddamar da yakin neman zabensa na shekarar 2024 a ranar 20 ga watan Janairun 2021, wato ranar da za a rantsar da zababben shugaban Amurka.