Amurka ce ta jagoranci sulhu tsakanin Daular Larabawa da Isra’ila inda a ranar Alhamis, shugaba Trump ya sanar da cimma yarjejeniya tsakanin ƙasashen biyu kan ɗage haramcin wayoyin salula tsakaninsu.
A baya dai, mutumin da ke a Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ba zai iya kiran wanda ke a Isra’ila ba.
Ministan sadarwa na Isra’ila, Yoaz Hendel, ya yi murna kan matakin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan ta ɗauka na cire wannan takunkumi, kuma ya ce ƙasashen za su amfana ta hanyar tattalin arziƙi.
A wata yarjejeniya da ƙasashen kuma suka saka wa hannu, sun amince kan wani batu da ke da alaƙa da gudanar da bincike kan cutar korona