Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tsohon Shugaban Nijar Tandja Mamadou ya rasu ranar Talata yana da shekara 82.

Tsohon shugaban ya mutu ne a Yamai, babban birnin ƙasar.

“Baba Tandja” kamar yadda ‘yan Nijar ke kiran sa, tsohon soja ne kuma yana cikin rukunin sojojin da suka yi juyin mulki a shekarar 1974.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya yi ta’aziyya ga iyalansa da kuma al’ummar Nijar.

Za a yi makoki na kwana uku a ƙasar baki ɗaya, kamar yadda wata sanarwa daga fadar Shugaba Mahamadou Issoufu ta bayyana.

Ya mulki Nijar daga Disamban 1999 zuwa Fabarairun 2010.

An tumɓuke shi daga shugabancin Nijar a wani juyin mulki sakamakon ya nemi yin tazarce biyo bayan kammala wa’adi biyu a karagar mulki.

Tandja ya shirya zaɓen raba gardama a 2009 domin gyara kundin tsarin mulki, wanda ya ba shi damar ci gaba da mulki na tsawon shekara uku, yana mai cewa ‘yan ƙasa ne suka nemi ya yi hakan domin ya jagoranci haƙo ma’adanin uranium da kuma man fetur.

Tuni da ma Tandja Mamadou wanda tsohon shugaban jam’iyyar MNSD Nassara ne, ya daina shiga al’amuran siyasa.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *