Tasha wani waje ne dake da dogon tarihi a rayuwar matafiya tun kafin zuwan Turawa inda matafiya kan taru domin daura aniyar tafiya fatauci, sada zumunta ko yawon bude ido kafi zuwan mota kasar hausa matafiya kan taru a waje guda kafin tashi zuwa inda zasu, zuwan mota sai alamuran sufuri ya karu inda gwamnati ta kirikri Tashar Mota tare da yiwa tsarin faskwarima da yayi daidai da zamani inda tsarin ya haifar da karuwar tashoshin mota a fadin kasar nan cikin harda jihar Kano.
Tashar Motar Rijiyar Zaki na daya daga cikin tashshin mota da sukayi shura a jihar kano wajen samun masu tafiye tafiye zuwa sassan kasarnan musamman na Bangaren Arewa Maso yamma,
Idris Badamasi City Boy shine Shugaban Tashar Rijiyar Zaki a tattaunawatsu da wakiliyar Express Radio Online ya bayyana mata cewar sabanin yadda alumma ke kallon tasha na waje dake tattatare da fitsararru Badamasi yace a’a Tasha duniya ce ! Idan aka dubi yadda alumma daban daban na ciki da wajen kasa ke amfani da ita tare da samun biyan bukata, yakara da cewa bayan amfanin alumma wajen sufuri da tafiye tafiye tashar mota wajene da ke samar da sana’un dogaro da kai na Halali idan akai duba da irin dumbin mutane da suke amfana da ita waje saye da siyarwa a kullum,
Kananan sanaoi irin su Shayi,abinci, ruwan sha,saida rake, kunun zaki, zomo, gyada, da sauran sanaoi na cin gajiyar tasha tare da taka rawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasa da mutane da dama a tashoshi,
Idris Badamasi yace a tashar su akalla suna da matasa sama da dubu daya wadanda suke neman na kansu ba tare da taimakon kowa ba.
Hakazalika samun fasinja a tasha yana samuwa lokaci lokaci ne domin kuwa anfi samun fasinja a lokacin kaka da sabanin lokacin damuna domin kuwa yawancin fasinjojin su tafi gida domin yin noma.
Duba da irin yawan matasan dake kai komo a ciknin tashar ya zama wajibi gwamnati ta shigo cikin harkar wajen basu tallafin daya kamata domin su cigaba da dogoro da kansu.
Idris Badamasi City Boy yayi kira da gwamnati ta zamanantar da harkokin Tasha ta wurin yi musu tituna a cikin tashar tare kuma Samar musu Masaukin Baki domin bakin direbobi da fasinjoji da suke shigowa cikin tashar da dare kuma basu da inda zasu sauka zuwa safiya.
Mai rahoto Fatima Binta Mohammed