Daga-Abubakar Sale Yakub
Dubun dubatar al’ummar musulmi mabiya Darikar Qadiriyya suke gudanar da zagayen kattamar mauludai tare zikiri da hailala a cikin kwayar Birnin Kano.
Tawaga tawaga ta matasa daga unguwanni daban daban dake cikin Birnin Kano da wajenta suke tafe suna zikiri da hailala, duk kan sun sanye da fararen kaya da rawani da hula ruwan goro.
Sun kuma tasone daga Masallacin Asahabul Khafi dake unguwar Gwale filin Mushe inda suke zagaye a cikin Birnin kano.
Sheik Abduljabbar Nasir Kabara, shine Babban jagoran tafiyar wanda yake jan ziriki da hailala duka dai dan dora matasa a tafarki na addinin Islama da son Manzon Tsiri Annabi S.A.W.
Taron dai kammatar Mauludai ana gudanar dashine duk shekara, wanda abanama yake wakana tare dafawar jami’an tsaro, wadan sukewa tawagar Rakiya.
Al’ummar musulmi daga ko’ina suke halatar wannan taron kammala taron mauludai na mabiya darikun sufaye suke gudanarwa a akowacce shekara.