Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Taron bunkasa cigaban matasa masu nakasa na jihohin arewa maso yamma, ya zama abin kwatance duba da yadda nakasassun matasan da suka fito daga yankin suke murnar shirya taron da ya zamo irinsa na farko a tarihi,

Shirin da maaikatar matasa da bunkasa wasanni ta tarayya da hadin gwiwar gwamnatin jihar kano ta shirya ya samu halartar babban sakatare na maikatar ta tarayya Mr Gabriel Aduda a madadin minista Sunday Dare wanda yace gwambatin tarayya ta damu kwarai da halin da masu bukata ta musamman kedasu shiyasata kirkiro wata hukuma da zata dauki gabaren kulada bunkasa cigaban masu bukata ta musamman a fadin kasarnan,

Shikuwa gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda kwamishinan matasa da bunkasa wasanni Kwamared Kabiru Ado Lakwaya ya wakilta wanda kuma ke matsayin mai masaukin baki godewa gwamnatin tarayya yayi bisa amincewar ta na bawa jihar damar daukar nauyin shirin, inda yace tuni jihar tayi gaba tsakanin jihohin kasarnan wajen tallafawa masu bukata ta musamman duba da irin rawar da take takawa wajen samar musu da hanyoyin bunkasa rayuwar su data iyalansu bisa sahalewar gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje,wanda a koda yaushe ke kokarin kyautata rayuwar su inji Kwamred Kabiru Ado lakwaya.ya kara da cewa kimanin matasa 20 daga cikin 90 dake halartar taron da dukayi nasara a baje kolin fasaha da badirarsu zasu sami kyaututka da zasu bunkasa sanaarsu yayin da sauran suma zasu rabauta da wasu kyautuka da zasu tallafi rayuwarsu.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *