
Shugaban Kungiyar Cigaban Mazauna Tishama Aminu Abdu Zakari, ya firta hakan a wajen taron rabawa Jama’a Marassa karfi kayan abinci da kudi naira dari biyar, domin ragemusu radadin rayuwa.
Aminu Abdu, yace “taimakon marassa karfi zai sanya Allah ya ye wannan masifa ta annobar coronavirus a Najeriya da Duniya baki daya.
Da yake Jawabi a wajen taron Dagacin Hotoron Arewa Yahaya Yakubu, ya bukaci alummar yankin dasu had a kai su kuma tallafawa wadan da basu da karfi.
Wasu da suka amfana da talalfin sun bukaci madawata da kamfanoni da Kungiyoyi dasuyi koyi da wannan aikin jinkai.