Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A wani mataki na maida martani kan hare haren da Turkiya ke kaiwa kan sojojinSyria, Majalisar dokokin kasar ta kada kuri’ar tuhumar Turkiya da aikata kisan kiyashi kan Armeniyawa miliyan 1 da dubu 500 a tsakanin shekarun 1915 zuwa 1917.
Majalisar dokokin kasar ta Syria ta ce Turkiya ta aikata kisan kiyashin ne karkashin daular Ottoman a farkon karni na 20.
Mahukumtan Erevan baban birnin kasar Armeniya dai, na zargin gwamnatin Ottoman da tisa keyar dubban Armeniyawa zuwa Syria, wadanda ta halaka mafi akasarinsu, wadanda suka tsira da rayukansu kuma, ta killace su a wasu sansanoni dake yankin arewa maso yammaci da kuma gabashin kasar ta Syria.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *