Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kungiyar yan jaridu marubuta labarin wasanni ta jihar kano ta nada Shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta jihar kano Sharu Inuwa Rabiu Ahlan a matsayin uban kungiya,

A wani kasaitaccen biki da aka gudanar a dakin taro na hukumar wasanni ta jihar kano dake club road shugaban kungiyar Zaharadeen Sale yace nadin Ahlan a matsayin uban kungiyar ya biyo bayan irin goyon bayan da yake bawa kungiyar a koda yaushe,

Da yake mika takardar tabbatarwa ga Sharu Rabiu Ahlan Shugaban kungiyar yan jaridu ta kasa shiyar jihar Kano Comred Abbas Ibrahim ya yabawa kungiyar marubuta labarin wasanni bisa hangen nesan su, kana ya taya sabon uban kungiyar murna da fatan alheri,

Da yake jawabi Jim kadan bayan karbar mukamin Sardaunan Makaman Bichi ya godewa kungiyar marubuta labarin wasannin tare da sauran yan Jaridu bisa goyon baya da gudummawa da suke bashi tun yana matashin Dan Wasa har zuwa yanzu inda yace bazai taba mantawa ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *