
Dakarun Sojin Najeriya biyu ne aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar coronavirus bayan gwajin da aka yi musu a Monguno, jihar Borno, kamar yadda jaridar Sahara reporters ta tabbatar.
Sojojin biyu da suka dawo sansaninsu bayan sun dawo daga hutu, an killacesu ne a sashi na uku na hedkwatarsu don lura dasu tun ranar Asabar, 28 ga watan Maris, 2020.
Ba a tabbatar da cewa ko hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta hada da sojojin ba a cikin jimillar wadanda aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar a kasar nan ba.
Tun farkon samun bullar kwayar cutar coronavirus a Najeriya ta hannun wani dan kasar Italiya, an tabbatar da samun kwayar cutar a jihohin Najeriya 12.