Hedikwatar rundunar tsaro ta sojojin Najeriya ta ce dakarun rundunar musamman ta Operation zaman Lafiya Dole sun kashe mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da dama a kusa da dajin Sambisa da ke Jihar Borno.
A wata sanarwa da ta wallafa a yau Asabar, rundunar ta ce jiragen yaƙinta sun kai hari Laraba, inda suka yi nasarar lalata wata tankar yaƙi ta mayaƙan amma ba ta faɗi adadin waɗanda ta kashe ba.
Kazalilka ba ta bayyana rauni ba ko halaka daga ɓangaren nata dakarun.
A ‘yan kwanakin nan ne Boko Haram ta gayyaci ‘yan fashin da ke aikata mugayen laifuka a yankin arewa maso yamma domin su yi aiki tare a cikin wani bidiyo mai tsawon minti 13 da kungiyar ta fitar.
A makon nan ne shugabannin rundunar tsaron suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari, inda rahotanni ke cewa shugaban ya ja kunnensu da cewa sai sun zage dantse.