Laakari da yadda tsarin mallakar bindiga yake a hukumance da yadda bindigar ta yawaita a hannun yan taadda tsohon tubabben shugaban yan bindiga, Auwal Daudawa, ya bayyana cewa samun bindiga sauki gare shi kamar yadda ake siyan burodi.
Daudawa ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da Daily Trust.
Da aka tambaye shi yadda ya ke samun bindigu, ya ce: “Akwai su barkatai. Samun bindiga ba abu ne mai wuya ba. Kamar zuwa ne ka siya burodi.”
DUBA WANNAN: Hotunan ɗalibar da ta tafi makaranta da bindiga za ta harbi malamin da ya ce ta aske gashinta mai launi
Daudawa ya ce rashin adalcin da ya fuskanta a rayuwa ne ya saka shi ya zama dan bindiga.
“Saboda rashin adalci ne. Rashin adalci kamar a ce kana da kayanka kana kulawa da iyalanka kawai sai gwamnati ta aike da jami’anta su kwashe maka dukkan abinda ka mallaka yayin da ina da iyalai da zan kula da su.
“Mai zan yi? Kasa ake tsammani zan ci? Ina ga shanu da na gada daga iyaye na amma an aiko da jami’ai sun kwace sannan suka kawo ni nan Gusau. Don haka na tunkari kallubalen.”
Da rashin adalcin da ya fuskanta, Daudawu ya kara da cewa jami’an tsaro sun kwace masa shanunsa a Zamfara. Hakan yasa ya siyar da sauran abinda ya mallaka ya siya bindiga.