Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A ranar 17 ga watan Disamba, 2020, shugabannin PDP na kasa, suka tabbatar da zaben da aka shirya a kananan hukumomi 44 da ke jihar.

Jam’iyyar ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar a ranar Alhamis, hakan na zuwa ne a lokacin da ake samun sabani a reshen Kano.

Jam’iyyar tace ta gamsu cewa an gudanar da zaben shugabanni na ranar 12 ga watan Disamba, 2020, ba tare da an samu wata matsala ba.

Jawabin yace: “NWC ta na farin cikin sanar da cewa an shirya zabe sumul kamar yadda ka’idoji da sharudan jam’iyyar PDP su ka tanada.”

Wannan mataki da majalisar NWC ya samu daurin gindi a karkashin doka kamar yadda sashen dokar jam’iyyar na 2017 ya bada dama.

Haka zalika jam’iyyar tace hukumar INEC ta sa ido a lokacin da aka zabi sababbin shugabannin.

“Kamar yadda kuma kwamitocinmu na sauraron kara suka bada rahoto, ba a samu wani korafi ba, wanda ya tabbatar da zaben shugabannin.”

Mun samu labari cewa uwar jam’iyyar PDP mai hamayya a kasa ta tabbatar da zaben shugabannin da aka yi kwanan nan a Kano.

NWC ta ce: “Sabon shugaban jam’iyya na Kano, Shehu Wada Sagagi, zai rike kujera na tsawon shekaru hudu kamar yadda dokarmu ta tanada.”

“Uwar jam’iyyar PDP ta tabbatar da zaben sababbin shugabanni a bangaren reshenmu na jihar Kano. “inji majalisar NWC ta bakin Kola Ologbondiyan.

Idan za ku tuna, jiya ne bangaren Aminu Wali wanda su ka shiga kotu da barin Rabiu Kwankwaso, su ka kori tsohon gwamnan daga jam’iyyar.

Bangaren na Wali ya na ikirarin cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya karya wasu dokokin kundin tsarin jam’iyyar tare da shirya mata zagon-kasa a Kano.

A karshen jawabinta, jam’iyyar PDP ta yi kira ga ‘ya ‘yanta su hada kai domin ceto mutanen kasar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *