Shugaban ‘yan ta da ƙayar bayan Sudan da suka yi yaƙi a yankin yammacin Dafur shekara 20 baya, ya musanta aikata laifukan yaki.
Ali Kushayb yayi magana ne a karon farko da bayan gurfanarsa gaban kotun manyan laifuka ta duniya a nek,
Bbc tace shi ne shugaban tawagar Jamjaweed – dan tada kayar bayan gwamnati mai hadari, wanda suka aikata cin zarafi iri-iri ga fararen hula a kasar.
An ba da umarnin kama shi ne shekara 13 baya, tare da jerin zarge-zarge 50 da ake tuhumarsa da su, ciki harda laifukan yaƙi kan fararen hula, da suka hadarda kisan kai da fyade da kuma azabtarwa.
An zagaye shi ne a makon jiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, in da yake buya tun watan Fabrairu, lokacin da Sudan ta sanar cewa za ta mika duk wadanda ake zargi gaban kotun manyan laifuka ta duniya.
Shi ma tsahon shugaban kasar Omar al-Bashir kotun na nemansa ruwa a jallo.
An kashe kusan mutum 300,000 yayin rikicin na Dafur kuma kusan mutum miliyan 2.5 sun tsere daga muhallansu.