Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban Ghana Nana Akufo Addo ya killace kansa tsawon makwanni 2 saboda coronavirus, duk da cewa gwaji ya nuna baya dauke da cutar.

Ministan yada labaran Ghana Kojo Oppong Nkrumah, ya ce shugaban ya dauki matakin ne domin rigakafi, bayan da gwaji ya nuna wani makusancinsa ya kamu da cutar ta corona.

Kawo yanzu Ghana na da jumillar mutane dubu 19 da 300 da suka kamu da wannan cuta, daga cikinsu kuma 117 suka mutu.

A karshen mako ne dai mataimakin ministan kula da kasuwanci a kasar ta Ghana Hon. Carlos Kingsley Ahenkorah yayi murabus, saboda karya ka’idar killace kansa da yayi, wanda daga bisani gwaji ya nuna ya kamu da cutar ta coronavirus.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *