Shugaba Muhammadu Buhari ya yi maraba da sakin daliban makarantar GGSS Kankara a jihar Katsina, mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.
Buhari ya siffanta cetonsu a matsayin babban sauki ga iyayensu, kasar, da kuma duniya gaba daya.
A gajeren jawabin da ya yi bayan sanar da sakin yaran, Buhari ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda ke da hannu wajen wannan nasara.