Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rikici tsakanin kabilu daya kunno kai tsakanin alummomi daya kunno kai a baya bayannan tsakanin hausawa da kabilar yarabawa ya sanya Shugaba Muhammadu Buhari alkawari cewa ba zai bari wata kungiyar addini ko kabila ta jawo fada da rikicin kiyayya da juna a Najeriya ba.

Shugaban kasar ya fitar da jawabi ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, a ranar Lahadi, 14 ga watan Fubrairu, 2020 ta shafin Twitter.

Fadar shugaban kasar ta fito ta yi tir da rikicin da wasu bangare na kasar su ke neman su tada a Najeriya.

Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da abubuwan da ke faru wa a kudancin Najeriya inda ake hallaka mutanen wasu kabila, a garin Shashsa, jihar Oyo.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashi gwamnatinsa za ta kare dukkan kabilu da addinai; masu rinjaye ko marasa rinjaye, kamar yadda tsarin mulki ya daura mata nauyi.”

Jawabin ya cigaba: “Shugaban kasa ya na gargadi cewa gwamnatinsa ba za ta bari wasu kungiyoyin addinai ko kabilu su tado da rikici da ta’adi a kan sauran jama’a ba.”

A jawabin da ya fitar jiya da daddare, Mai girma shugaban kasar ya tabbatar da cewa zai kawo karshen wannan kashe-kashe domin ganin abin bai yadu zuwa sauran wurare ba.

“(Buhari) ya yi kira ga shugabannin addini da gargajiya, har da gwamnoni da zababbun shugabanni a kasar, su hada kai da gwamnatin tarayya na ganin an samu zaman lafiya.”

Hakan na zuwa ne bayan kashe-kashen da aka yi sun jawo rashin rayukar Hausawa da dukiyoyinsu a Oyo.

Kwanakin baya kun ji cewa kungiyar Miyetti Allah ta amince da rajistar makiyaya, ta bukaci a raba masu kati ta yadda za a rika banbance nagari da miyagu.

Shugabannin Fulani sun sha alwashin bankado duk wani Makiyayi da ya ke yawo da makamai.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), na reshnen Ekiti, Adamu Abache, ya goyi bayan matakan da gwamnati ta zo da su.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *