
Shugaba Buhari ya ce dangane da Kano. “Na ba da umarnin tilasta rufe Kano gaba daya tsawon mako biyu, hakan kuma na farawa ne daga nan take.
Gwamnatin tarayya za ta tura dukkan mutanen da kayayyaki da suka wajaba don tallafa wa jihar wajen shawo kai da killace annobar da ma kare jihohi makwabtanta daga kasadar sake bazuwar cuta.”Muhammadu Buhari ya ce yayin da suke ci gaba da kaifafa kokarin kai dauki a cibiyoyin jihar Legas da ma na babban birnin tarayya, ya kuma damu kan munanan al’amuran da ke faruwa a Kano cikin ‘yan kwanakin nan.
A cewarsa: “Duk da ana ci gaba da gudanar da zuzzurfan bincike, amma sun cimma shawarar tura karin ma’aikata da kayan aiki da tallafin kwararru don karfafawa da mara baya ga kokarin gwamnatin jihar nan take.”
Ya ce Kano, da ma sauran jihohi da dama da ake samun sabbin masu kamuwa da cutar korona, binciken farko-farko ya nuna cewa irin wadannan mutane galibi sun kamu ne sakamakon tafiya daga wata jiha zuwa wata da kuma yaduwar cutar a tsakanin al’umma da ke karuwa.