Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargaɗi shugabannin ƙungiyar ci gaban tattalin arzikin ƙasashen Afirika ta Yamma ECOWAS kan tsawaita mulkinsu yana mai cewa hakan babban hatsari ne.
Ya bayyana haka ne a Jamhuriyyar Nijar a yau Litinin inda shugabannin suka haɗu don tattaunawa kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi yankin.
Taron na kwana ɗaya, kuma shi ne irin sa na 57 kuma an gudanar da shi ne a Yamai, babban birnin ƙasar.
Taron ya tattauna kan yanayin da ake ciki a Mali bayan juyin mulkin da soji suka yi wa Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ranar 18 ga Agusta lamarin da ya sa ECOWAS ta sanya wa ƙasar takunkumi.
Shugabannin ƙasashen Najeriya da Senegal da Cote d’Ivoire da kuma Burkina Faso na daga cikin mahalarta taron.
Wata sanarwa da Malam Garba Shehu, kakakin shugaban Najeriya ya fitar ranar Litinin da la’asar ta ce Shugaba Buhari ya bukaci takwarorinsa na ECOWAS su daina tsawaita mulkinsu domin hakan “yana zama silar matsala”.