Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban jamaatu ahli sunnati. liddaawati wal jihad da akafi sani da kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da sabon sako game da sabbin manyan hafsoshin tsaro

– A sakon mai tsawon kimanin mintuna 9, Shekau ya shaidawa sabbin shugabannin sojojin cewa babu wani abu da za su iya yi da magabatansu ba su yi ba

– Bayan ambaton sunayensu da ayyukansu, Abubakar Shekau ya yi kira gare su da su tuba su rungumi musulunci

Abubakar Shekau, shugaban tsagi guda na kungiyar Boko Haram ya fitar da sabon sautin murya inda ya yi magana game da nadin sabbin manyan hafsoshin Najeriya, inda ya ce babu wani abu da za su iya tabukawa da magabatansu ba su yi ba a yaki da ta’addanci a arewa maso gabas, HumAgle ta ruwaito.

A sautin da ya fitar mai tsawon mintuna tara da dakika 56, Shekau ya ce ya ji labarin yi wa tsaffin manyan hafsoshin tsaron murabus da maye gurbinsu da sabbi amma ya yi kira garesu su amshi musulunci

A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da yi wa tsaffin manyan hafsoshin tsaron murabus tare da maye gurbinsu da sabbi.

Kungiyoy da mutane da dama sun dade suna kira da shugaban kasar ya sauya manyan hafsoshin tsaron.

A cikin sabon sautin muryar da Shekau ya fitar, ya ambaci sunayen manyan hafsohin tsaron daya bayan daya da ayyukansu sannan ya yi kira garesu da su tuba domin babu wani abu da za su iya yi domin tarwatsa kungiyarsa.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *