Shahararren ɗan ƙwallon duniya Diego Maradona ya mutu yana da shekara 60.
Ya rasu ne ranar Laraba sakamakon bugun zuciya.
An yi nasarar yin tiyata a ƙwaƙwalwar tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafar na Argentina kuma kocinta a farkon watan Nuwamba.
Daga nan ne aka sanar cewa za a yi masa magani kan jarabar shan barasa.
A matsayinsa na ɗaya daga cikin shahararrun ‘yan ƙwallon ƙafar duniya, Maradona shi ne kyaftin na Argentina lokacin da ta lashe Kofin Duniya a 1986, inda ya murza leda mai ƙayatarwa.
.A saƙon da ta wallafa a shafin Twitter, hukumar ƙwallon ƙafar Argentina ta bayyana “matuƙar baƙin cikinta bisa mutuwar gwarzonmu”, tana mai ƙara wa da cewa: “Za ka ci gaba kasancewa a zukatanmu.”
Ɗan ƙwallon Argentina da Barcelona Lionel Messi ya bayyana alhininsa bisa rasuwar Maradona, yana mai cewa shi “Mahadi ne mai dogon zamani”.
“Wannan ranar matuƙar baƙin ciki ce ga dukkan ‘yan ƙasar Argentina da masu son ƙwallon ƙafa,” in ji Messi. “Ya bar mu amma yana raye saboda Diego abin tunawa ne.”