Sauran yan Najeriya 419 da suka makale a kasar Saudiyya sun dawo ranar Juma’a 29 ga Junairu, bayan sahun farkon mutane 384 da suka dawo ranar Alhamis.
Wadanda suka dawo sun hada da maza 126 da mata 293, da yara, kuma sun dira a tashar jirgin saman Nnamdi Azikwe cikin jirgi mai lamba SV-3413 misalin karfe 11:57 na safe.