Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

 2020

Getty

Saudiya ta ce zata cire dokar kulle a fadin kasar tare bude harkokin kasuwanci nan da ranar Lahadi, a wani matakin sassauta dokar duk da cewa ana kara samun masu kamuwa da cutar.

Za a janye dokar kullen daga karfe 6:00 safe na kasar tare da barin ci gaba da sallah a masallatai da bude kasuwanni a kasar.

Jiragen kasa da kasa za su ci gaba da kasancewa a dakace, an kuma hana taron sama da mutum 50 a waje daya, in ji gwamnatin kasar.

Har yanzu hukumomin kasar ba su bayyana ko za a yi aikin hajji wannan shekarar ba, wanda kusan mahajjata miliyan biyu ne ke zuwa ko wacce shekara a fadin duniya.

Har yanzu ana samun masu kamuwa da cutar korona a Saudiyya, wadda ke da sabbin masu cutar da suka kai 3,941 cikin sa’a 24, wanda ya kai adadin masu cutar a kasar 154,233.

Har zuwa ranar Asabar, kasar na samun masu cutar korona sama da 4,000 kwana shida a jere.

Akwai wadanda suka mutu 1,230 ya zuwa yanzu a kasar, tare da karin sanar da mutum 46 a ranar Asabar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *