
Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ya ce sun karbi ‘yan Najeriya mutum 292 da suka makale a Saudiyya.
Ministan wanda ya wallafa bayanin a shafinsa na Twitter ya ce jirgin Saudiyya ne ya kai mutanen filin jirgin sama da ke birnin Abuja a daren Talata.
Ya kara da cewa mafi yawancin mutanen da aka mayar da su Najeriyar mata ne masu shayarwa da kananan yara.
Sai dai ya ce yanzu haka an killace su a otal har zuwa makonni biyu kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanadar wajen gane ko suna dauke da cutar korona ko a a.
Wannan ce dai tawaga ta baya-bayan ta ‘yan Najeriyar da suka makale a kasashen waje a zamanin korona.
Kusan dai wannan ne karon faro da wata kasa ta mayar da ‘yan Najeriya ga kasarsu sakamakon annobar korona da ta katse wa matafiya da dama hanzari.
A baya dai Najeriya ta yi jigilar ‘yan kasar tata daga Burtaniya da Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa.