Daga-Abubakar Sale Yakub

Sarkin Oman Haitham bin Tariq Al-Said a ranar Lahadi, ya bayar da umarnin kafa kwamiti da zai tun kari tabarbarewar tattalin arziki da kasar ta tsinci kanta a ciki sabo da cutar corona acewar kafar yada labaran kasar.
Kasar Oman dai karamar kasace dake fitar da Manfetur dake da makotaka da kasashen yankin gulf, ta shiga cikin tsaka mai wuya sabo da cutar corona abin daya karya farashin man fetur a kasuwar Duniya.
Ministan cikin gidan Oman shine shugaban kwamitin wanda zaiyi nazarin yadda tattalin arzikin kasar zai farfado cikin kan kanin lokaci.