Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira da masu rike da madafin iko da mawadata da su kara taimakawa fannonin lafiya domin magance matsalolin da al’umma suke fuskanta a bangaren lafiya.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin bude cibiyar kula da marasa lafiya wace babban akawunta na kasar nan Ahmad Idris daneji ya samar a cikin unguwar daneji dake karamar hukumar birni.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce samar da irin cibiyoyin zai kawar da cinkosan da ake samu a asibitocin gwamnati.

Yakuma yabawa babban akawuntar kasar nan Ahmad Idris bisa namijin kokarin da yayi wajan samar da cibiyar kula da marasa lafiyar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *