
Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi wa fursunoni 2600 afuwa a wani mataki na hana cunkoso a wannan lokaci da kasar ke yaki da annobar coronavirus.
Sai dai sakin fursunoni ya janyo ce-ce-kuce tsakanin masu kare hakkin bil adama, ko da ya ke wasu sun yaba da matakin.
Sanata Shehu Sani, da ke fafutukar rajin kare hakkin bil adama ya ce idan akayi la’akari da cunkoson gidajen yarin Najeriya, kamata ya yi a ce kusan kashi 50 na fursunoni aka sallama.
Tsohon Sanatan da shi ma a baya ya taba zama a gidan yarin kasar, ya ce halin da gidan yarin kasar ke ciki ya wuce misaltuwa, akasari zama ake a cakude babu walwala.
Ya ce ”Duk abubuwan da ya kamata a ce akwai a kurkuku babu su, sannan tsarin irin na turawan mulkin mallaka ne babu wani abu sabo a ciki”.
Sannan ” Hatta dokokin gidan yarin ba su sauya ba, da tsarin cin abinci, haka babu sabbin gine-gine.”