Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tsohon dan majalisa, Sanata Shehu Sani, ya baiwa tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II wasu shawarwari masu muhimmanci.

Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya cire Sanusi daga kan karagar mulki a ranar Litinin 9 ga watan Maris kan zargin da da rashin yi wa gwamnati biyayya.

Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Asabar 14 ga watan Maris, Sanata Shehu Sani ya shawarci tsohon sarkin kada ya yarda a ja shi ya shiga siyasa.

Ya kuma shawarci sarkin da kada ya bari wasu kungiyoyi ko mutane su yi amfani da shi domin cimma matsayarsu.

Ya rubuta, “Ya kai Sanusi,

Ka huta sosai tare da iyalanka yanzu da babu nauyin sarauta a kan ka; Ka guji mutanen da ke kokarin tsinduma ka a cikin siyasa kuma kada ka bari ayi amfani da kai.

Zama jarumi kawai ya isa, su je su nemi shahidin su a wani wuri.”

A baya, Sanatan ya yi tsokaci a kan mukaman da gwamnan jihar Kaduna,Nasir El-Rufai ya bawa sarkin bayan an sauke shi.

Kasa da awanni 24 da sauke shi gwamnan ya nada Sanusi shugaban gudanarwa na KASU da kuma mamba na masu bayar da shawara na KADIPA.

A yayin da wasu ke yaba wa gwamnan saboda nuna goyon baya ga tsohon abokinsa, Sanata Shehu Sani bai yi wa abin irin wannan kalon ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *