Tsohon Danmajalisar wakilai mai wakiltar Birnin kano da kewaye Dr Danburam Abubakar yace halin matsin tattalin arziki da duniya ta shiga sakamakon cutar Covid 19 ya bude wani sabon babi ga masana tattalin arziki a fadin duniya na fara tunanin wata mafita da kaucewa irin halin da Duniya ta tsinci kanta,
Tsohon Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar kano kuma masanin tattatalin arziki yace hanya daya da zaa bi da kaucewa irin halin matsananci tattalin arziki da talaucin a yan Najeriya suka tsunduma shine, shugabanci na gari da zai yi duba na tsanaki tare da bijiro da hanyoyin dogaro da kai masu dorewa,
A tattaunawarsa da wakilin mu Dr Daburan Nuhu yace ya zama lallai a samu tsarin da zai tabbatar da samu hanyoyin samar da ayyukan yi na kashin kai tare da wayar da kan yan kasa mahimman ci da alfanun kananan sanaoi wadanda aka gada kamar yadda kasashen da sukaci gaba suka rike har suka bunkasa,
Da yake karin haske kan kananan sanaoi Danburan Nuhu ya bada misalin da jihar kano inda yace kowa yasan yadda ta bunkasa wajen sarrafa fatu da kirgi, fiye da shekaru 300 amma har yanzu an kasa tabbatarda ganin wannan sanaa ta mamaye jihar, an kasa bunkasata yadda na baya zasuyi kwadayi da zumudin shiga sanaar,
Kan yadda zaa bunkasa irin wadannan sanaoi har sukai ga zama manyan masana’antu Farin Jakada cewa yayi kasashen da sukaci gaba, baa bukatar chunkushewa waje daya na tarin sanaoi barkatai a maimakon haka sai dai kowane gari ya zama kwararre akan abu daya da duniya zata nema,inda ya bada misali ga kasar China, inda yace duk da yadda yawansu yake bai hana musu damar yin ilimi na fannoni da dama ba da suka tabbatar duniya zata bukaceshi nan da shekaru da yawa ba ,inda sukai ta binciken yadda zasu kware tare da mamaye duniyar da ilimin kimiyya da fasaha ba , ya kara da cewa a china ne zaka samu gari (FITILA) kawai suke kerawa duk yankin aikinsu kenan kuma shi suka kware kuma duk kasar ananne kawai ake yin fitila,yayin da a wata jihar kuma (KWAN FITILA) kawai ake kerawa, wasu Noma na abinci wasu na abin Marmari wasu kayan sawa, wasu Waya da abubuwa da dama da suka rabasu Jahohi daban daban dan samarwa da mutanensu abin dogaro da gaba,
Da yake amsa tambaya kan yadda Najeriya ya kama ta zama tsohon kwamishinan cewa yayi akwai arziki mai tarin yawa da yafi na kowace kasa a duniya amma rashin kishin kasa da shugabanci na gari ya hana yin amfani da damar da Allah ya bamu na arzikin da yawan da muke dashi na ganin munci moriyar arzikin,sannan uwa uba rashin tsari da tattalin ga karancin aikin da sani, kasala ,kiwa da son samu a sauki.
Shin ko yaya zaayi maganin wadannan matsaloili da ka bayyana ?
Dr Danburan cewa yayi samar da Nagartaccen shugabanci kuma karbabbe ga daukacin alumma shine matakin farko na biyu kishin kasa ga shugabanni da mabiya da zai sanya kowa sanya kasar gaba da komai, sa samar da tsari mai dorewa kuma karbabbe ga jamaa, to wadannan ka iya zama danba da kuma Tushen samar da hanyar da zata fitar da mu daga halin matsin da muka tsinci kan mu,
Ba iya hirar kenan ba, nan gaba zamuji yadda kasahe ke dogaro da abin da suke dashi kafin suyiwo aro,