Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar Bichi kuma shugaban kwamitin ayyuka na majalisar Abubakar Kabir Abubakar Bichi yace samar da manyan dama damai wani abu ne da zai bunkasa cigaban tattalin arzikin yakin laakari da yadda alummar ke aiwatar da aikin gona a koda yaushe,

Da yake kaddamar da aiki fadada dama daman Garin Malikawar Garu dake mazabar Danzabura da Kungu a mazabar Fagwalo yace ya zama wajibi akansa daya samar da wadannan ayyuka dan samar da ayyukan dogaro da kai ga dinbin alummar dake yankin wadanda sukayi fice a sanaar noma, na rani da damina, inda ya kara da cewa wadannan Dam zssu zama abin alfahari ga daukacin Karamar hukumar Bichin duba da yadda zaa samar da abubuwan bukatu na yau da kullum tare da rage zaman matasa a inuwa ba bu aiki ko fita birane da zummar cirani,

Kabir Bichi a.k.a Abba yace wannan wani lokacine da zan yi duk msi yiwuwa dan ganin na samar da ayyuka da zasu taba rayuwa alumma kai tsaye, kowa yasan Garin Bichi wajen Saye da Siyarwa, Fatauci da Noma tun ba yanzu ba hakane ya sanyani maida hankalin wajen sake inganta harkokin mona daba da yadda aikin ke da tasiri wajen samar da aiki da rage zaman banza ga matasa,

Da yake karin haske kan yadda ayyuka ke kwarara a masarautar Bichi Abba cewa yayi yanzune muka samu damar da muke kokarin amfani da ita kamar yadda ya kamata fatan mudai alummar mu suci gaba da yi mana addua tare da bawa gwamnati hadin kai mu kuma zamuyi abin da zamuyi dan ganin mun kawowa alummarmu ayyukan da zasu san sunyi zaben daya dace,

Dan majalisar na tare da tawagar injiniyoyi da duk maikatan kamfanin da zasuyi wannan aiki da alummar garuruwan ke cewa sabuwar koface aka bude musu ta karuwar arziki a yankin.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *