Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban hukumar wasan kwallon kafa na babban birnin tarayya Abuja FCT Abba Muktar Mohammed yace majalisu dokokin kasa nada rawar da zasu taka na bada cikakkiyar kariya daga barazanar da filayen wasanni ke fuskanta na karewa a fadin najeriya.

A wata tattaunawa da wakilin express radio nigeria Abba Mukhtar yace samar da doka da zata kare filayen wasanni daga mamayar ginesu dan kasuwanci ne zai hana duk wani yunkuri na gwamnatoci ko hukumomi dasu suke na mallake filayen, da yake karin bayani kan mahimmancin da filayen wasanni ke dasu wajen bunkasar cigaban kasa da bukasa tattalin arziki Abba Muktar cewa yayi cigaban da manyan kasashen duniya suka samu da karfin tattalin arzikin wasu kasashen da sukaci gaba ya dogara ne ga kyawawan tsarin gudanarwa na harkokin wasanni inda kasashen ke ware wani kaso mai tsoka daga cikin kasafin kudin kowace shekara da bunkasa cigaban wasanni kamar yadda ake ware wa Lafiya, Ilimi, Tsaro da Sauran bangarori tun daga matakin kasa har Jihohi zuwa kananan hukumomi abin da shugaban kwallon kafar FCT yace shine mafita da zata share hawayen wadanda ke cikin harkar wasanni a fadin kasarnan,

Da yake amsa tambaya kan yadda samar da dokar zata tabbata Abba cewa yayi kawo iyanzu sun kafa wani kwamiti da zai kai wannan koke ga majalisar kasa domin neman daukin majalisar nayin wadannan dokoki dazasu kare martabar filayen wasannin da shugaban ke cewa sunada matukar tasiri wajen samar da makoma ga matasa masu shaawar wasanni da motsa jiki,

Da yake karin haske kan illar da rashin filaye ke haifarwa Abba Muktar cewa yayi wasanni ne kadai ke kare matasa daga shaye shaye da fadawa munanan dabiu duba da tasirin da motsajikin kedashi, inda yace ko hukumar wasan kwallon kafa ta duniya na kokarin dan ganin an samar da filaye managarta dan dasune za a iya zakulo yan wasa daga tushe da suke zama abin alfahari ga kasa da duniya baki daya ,

Dan gane da tsarin amfani kasafin kudi da ake warawa dan wasanni Abba cewa yayi ” Ba nace a debe kudi dan wasanni bane amma a tabbatar an sanya na wasanni kamar yadda doka ta tanadar wa bangaren a tsarin mulki kuma ayi amfani dasu kamar yadda ya dace” hakanne zai taimaka wajen bunkasa wasannin da yan wasan inji Abba Muktar din.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *