Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Sabbin alƙaluman masu kamuwa da cutar korona a Amurka ya yi matuƙar tashin gwauron zabbi inda ya zarta mutum dubu hamsin a cikin kwana guda.

Cutar ta harbi kusan mutum dubu goma a jihar Califonia kadai, abin da ya sa mahukuntan jihar sake ɓullo da wasu matakan daƙile annobar da aka janye a baya.

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan babban likitan da ke jagorantar yaƙi da korona a Amurka Dr Anthony Fauchi, ya yi gargadin cewa yawan masu kamuwa zai iya haura dubu ɗari a cikin kwana ɗaya.

Tuni dai gwamnan Califonia, Gavin Newsom, ya sake bijiro da wasu ɓangarori na matakan kulle, bayan sannu a hankali an riƙa sassauta su a jihar.

Gwamna Newsom ya sake ƙaƙaba matakan ne gabanin hutun ranar 4 ga watan Yuli, lokaicn da jami’ai ke fargabar samun ƙarin yaɗuwar cutar.

Wasu mazaunan birnin Los Angeles sun yi imani matakin yana kan hanya.

Ta ce “Abin takaici ne sake buɗe birnin nan, Ina jin hakan ya ɗan yi wuri. Kowa kawai yana ta fitarsa, suna zuwa kantunan barasa, suna zuwa taruka, suna zuwa gidajen abinci.

Shi ma Ben Smith ya faɗa wa BBC cewa: “Tabbas akwai wasu yankunan Califonia da mutane ba sa nuna damuwa game da halin da ake ciki”.

A cewarsa ba za ka ga mutane na sa takunkumi ba, ba za ka ga mutane na zama nesa-nesa da juna ba.

“Ko da yake ina jin a yankin Los Angeles mutane suna matuƙar yin abin da ya dace kuma mutane na ƙoƙarin zama cikin hattara yadda ya kamata musammam ma a yanzu da lamarin ke ƙara ƙazancewa, alƙaluma ke ci gaba da hauhawa,” in ji shi

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *