
Dan wasan Liverpool Sadio Mane zai iya komawa Real Madrid, a cewar dan wasan Senegal Keita Balde, wanda ya kara da cewa zai yi wahala Mane, mai shekara 28, ya ci gaba da zama a Anfield “har abada”. (AS, in Spanish)
Barcelona za ta sake taya dan wasan Brazil Neymar, mai shekara 28, domin ta dawo da shi daga Paris St-Germain. A shirye kungiyar take ta bayar da ‘yan wasan Faransa uku Samuel Umtiti, Ousmane Dembele da kuma Jean-Clair Todibo a matsayin yarjejeniya don karbo shi a daidai lokacin da suke fama da karancin kudi saboda annobar coronavirus. (Mundo Deportivo, in Spanish)
Ana sa ran dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 27, ya sabunta kwangilarsa a Manchester United kuma ana kallonsa a matsayin shugaba a kungiyar, a cewar dan jaridar Spaniya mai bayar da rahoto kan wasan kwallon kafa Guillem Balague. (Express)
Shahararren gola Gianluigi Buffon, mai shekara 42, ya amince ya tsawaita zamansa a Juventus. Hakan zai kasance karo na 19 da dan kasar ta Italiya ya ke sabunta kwantaraginsa a Turin. (Tuttosport, in Italian)