Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hukumomi a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum goma sha tara sannan fiye da gidaje dubu hamsin sun rushe sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliyar ruwa a sassan jihar.

Lamarin dai ya haddasa salwantar dukiyoyi a kananan hukumomi goma sha bakwai daga cikin ashirin da bakwai na jihar.

Al’amarin dai na zuwa ne bayan shafe makwanni ana tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya

Al’umomin garuruwan Babaldu da Shingurin da Samamiya da ke yankin karamar hukumar Birnin Kudu a jihar ta Jigawa, na cikin tsaka mai wuya sai dai lamarin ya fi muni a garin Shingurin wanda yanzu haka wani kogi da ya tumbatsa ya tasamma tashin garin ɗungurungum.

Baya ga rusa gidaje da lalata amfanin gona, har rasa rai wannan iftila’i ya haddasa inda wani matashi ya rasa ransa a garin na Shingurin.

Alhaji Umar Aliyu shi ne mahaifin matashin ya kuma shaida wa BBC cewa, yaaon nasa ya je kai taimako ne gidan kanin mahaifin nasa a nan ne kuma sai gini ya rufta masa anan ne kuma sai ya nitse a ruwan da ya zama kamar kogi.

Mahaifin matashin ya ce “Tun da ruwa ya tafi da shi ba a ganshi ba sai bayan kwana hudu, sannan aka gano gawarsa a wani gari can daban”.

A yanzu haka dai daruruwan iyalai ne wadanda suka tsira daga gidajen su suka sami mafaka a gidajen ‘yan uwa da makarantu da masallatai, yayin da wasunsu kuma suka ci gaba da zama a gidajen nasu duk da mamayewar da ruwan ya yiwa ciki da wajen gidajen nasu.

Malam Abubakar Garba Haske na daga cikin mutanen da suka rasa gidajensu ya kuma shaida wa BBC cewa, “Yanzu a makaranta nake kwana, muna da gidajenmu da wasu kayan abincinmu duk sun lalace, kai hatta tufafinmu duk sun lalace saboda tsabar ruwan sama wanda ya yi sanadin rushewar gidajenmu

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *