Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daga -Abubakar Sale Yakub

Rundunar ‘yansandan Jihar Anambra ta kubutar da wata Yarinya ‘yar shekaru goma da akai zargin an satotane daga Jihar Akwa Ibom, tare da sayar da ita akan kudi naira dubu dari (800,000) .

Rundanar ‘yansandan tace wadda aka sato ainihin sunan ta shine Favour Asuquo wadda aka sauya mata suna zuwa Faith Ezeukwu da wadan da ake zargi da sace a cewar iyayenta.

Maimagana da yawun rundunar ‘yansandan jihar SP, Haruna Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin Jaridar Daily trusta a birnin Akwa a ranar Lahadi.

A cewar SP Muhammad “Yarin yar tana da akalla shekaru 10 ana zargin an sacetane daga Jihar Akwa Ibom tun a shekarar 2018 tare da sayar da ita ga wasu ma’aurata akan kudi naira dubu dari takwas (800,000) ‘yan sanda dake sahin bincike na Ofishin ‘yansanda na 33 dake Onitsha suka kubutar da ita bayan samun bayanan sirri a ranar 21 ga watan Fabrairun 2020”.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *