Daga-Abubakar Sale Yakub
Rumfuna da Shaguna da dama suka kone kurmus sakamakon tashin wutar gobara a daren jiya a Kasuwar Kwanar Singa a nan Kano.
Wutar dai ta fara cine cikin dare, wadda ta kama rumfuna na langa langa da Shaguna, ta kuma haifar da asarar kayayyaki na miliyoyin Nairori.
Sai dai a hannu guda Tashar Express Radio, tagano cewar kusa da wajen da wutar ta tashi akwai rumfar mai sayar da Gas da mai Tuyar Kosai da Mai Shayi.
Wasu shedun gani da ido sunce “wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar domin idan an kawo wuta tana tararratsi a wajen”.
Har yanzu dai bamu samu damar jintabakin mahukuntan Kasuwar ta Kwanar Singa ba.
