Daga- Lamin Hassan

A safiyan nan hayaniya ta rincabe har da doke doke tsakanin ‘yan majalisun jihar Kano masu goyon baya da masu nuna adawa kan takardar korafi ga sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi na 2.
Hakan na zuwa bayan kakakin majalisar Abdul Aziz Garba Gabasa, ya karanto takardar korafin domin fara duba kan batun wanda hakan baiwa yan majalisar na jami’iyar PDP dadi ba har takai da doke –doke a tsakanin su.
A makon daya gabata ne majalisar dokoki ta Kano ta kafa wani kwamitin bincike kan mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi na II bisa korafin da wata kungiya ta kai mata na zargin yana gabatar da wasu dabiu n da suka saba da addini da al’adun jama’ar Kano.