Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Real Madrid ta shirya sayo dan wasan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 19, daga Borussia Dortmund a wannan shekarar da kuma dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 21, daga Paris St-Germain a shekarar 2021.

Kazalika, Real Madrid za ta fafata da Manchester United wajen yunkurin dauko dan wasan Ingila mai shekara 20, Jadon Sancho, wanda yake murza leda a Borussia Dortmund. 

Borussia Dortmund ta ware euro 40m domin sayo dan wasan Spain da Valencia Ferran Torres, mai shekara 20, wanda za a sayar a kan euro 100m kuma kwangilarsa za ta kare a 2021. 

Dole ne dan wasan Najeriya Odion Ighalo, mai shekara 30, ya amince a rage £200,000 na alawus-alawus da ake ba shi duk mako idan yana so a sauya zaman aron da yake yi a Manchester United zuwa na din-din-din daga ta Shanghai Shenhua, inda ake ba shi alawus da ya kai £300,000 duk mako. 

Chelsea za ta biya £5m idan tana son dauko dan wasan Derby County mai shekara 19 dan kasar Ingila Max Bird, wanda ya burge kocin Chelsea Frank Lampard lokacin da yake manajan kungiyar da ke buga gasar Championship. 

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *