Kasar Ivory coast (code Ivore )na cikin jimami bayan mutuwar fujia da firiministan kasa Amoudu Gon Koulibaly yayi a na tsaka da taron majalisar zartarwar kasar,
Gon Koulibaly wanda ake sa ran zai mulki kasar nan bada dadewaba yasha fama da ciwon zuciya, inda a baya bayannan ya je kasar faransa dan neman magani,
Shugaban kasa Alassane Quattara ya bayyana firiministan da cewa dan kishin kasane mai son ganin kasar ta samu cigaba, yace cikin alhini nayi rashin Da kuma aboki Mai son zaman lafiya da biyayya, kasarmu zata dade tana tunawa da wannan rana da tazo mana bazato,
Shugaban ya kara da cewa mutuwar koulbaly tazo lokacin da ake matukar bukatarsa