A wani kwarya kwaryan biki da aka gudanar a filin wasa na Ramcy dake rumfa college kungiyar kwallon kafa ta Ramcy gidan Sarki da akewa lakabi Royal Team a karon farko a tarihi ta kulla yarjejeniya ta shekara daya da wani kamfanin samar da ruwan sha na Korbit.
Da yake jawabi yayin kulla yarjejeniyar shugaban kamfanin Korbit Table Water Alhaji Garba Ahmed yace duba da irin Nasarori,bunkasa da kyawawan tsare tsaren kungiyar da yasha banban da suaran kungiyoyi a Jihar kano ya zama wajibi ga kamfaninmu ya kulla wannan yarjejeniya da bunkasa cigaban wasan da yan wasan a jihar kano da kasa baki daya,
Shikuwa shugaban kungiyar Aminu Abba Kwaru cewa yayi yarjejeniyar zata kawo saukin ga shugabannin kungiyar tare da zaburar da shugabannin, yan wasa da Magoya bayan kungiyar, da kuma sasu zage dantse Dan ganin kungiyar ta kai gaci kana yayi alkawarin taka rawar gani a wasannin su abin da zai sake kwadaitar da wasu kamfanonin yin gasa wajen daukar nauyin kungiyar dake bugawa a ajin matasa rukuni na daya na kasa NNWL,