Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daga-Abubakar Sale Yakub

Tawagar ma’aikatan Radiyon Katsina

General manager na Hukumar gidan Radio na jihar Katsina Alhaji Sani Bala Kabomo ya kai ziyara ga sabon Babban Daraktan Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Katsina Alhaji Suleiman Nuhu Kuki a offishinshi.

General manager da ya samu rakiyar Daraktochinshi ya shaida ma Babban Daraktan cewa sunzo ofishin nashi ne domin taya shi murna tare da yi mashi Addu’a Allah ya tsareshi ya kuma kawo mashi dauki wajen gudanar da aikin shi.

Alhaji Sani Bala Kabomo Wanda ya Babban Daraktan tabbacin bashi goyon baya da shawarwari wajen tabbatar da nasarar aikin Hajji a jihar katsina.

Ya kuma yi fatan zaya hada kai tare da Daraktocin shi da kuma sauran ma’aikatan Hukumar domin ciyar da Hukumar gaba musamman wajen tallafama Alhazai domin su sami Hajj Mabrur.

Da yake bayanin shi Babban Daraktan Hukumar Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ya gode da ziyarar tare da ba General manager tabbacin goyon baya da hadin kai tsakanin Hukumar da gidan Radio na jihar katsina da ma sauran kafafe na yada labarai.PRO PWBKT

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *