A ranar Talata ne Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta fitar da sanarwa kan cewa za ta ƙaurace wa zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a jihar.
A wata tattaunawa da BBC ta yi da Dakta Danladi Abdulhamid, wanda shi ne shugaban riƙo na jam’iyyar reshen jihar Kano, ya bayyana dalilan da ya sa jam’iyyarsa ta ɗauki wannan matsaya ta ƙaurace wa zaɓen.
Ya ce babban dalilin da ya sa suka ɗauki wannan mataki shi ne zargin rashin adalcin da ‘ya’yan jam’iyyar suke tunanin za a yi musu.
Dakta Ɗanladi ya bayar da misali da batun zaɓen 2019, inda ya ce “mun ci zaɓe aka murɗe, aka je kotu aka ƙara murɗe mu”. Ya ce yanzu haka suna da ‘yan takara a kowace ƙaramar hukuma, amma sakamakon sun ga ba za a yi musu adalci ba, shi yasa suka janye.
Haka kuma, ya zargi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Kano inda ya ce ita ma ba za ta yi musu adalci ba “domin abin da aka ce ta yi shi kawai take yi”.
“Mun lura mun ga, da a je a yi tashin hankali ko a zubar da jini, mu mutanen Kano da arewacin Najeriya muna neman zaman lafiya.”
BBC ta tambayi Dakta Danladi kan ko wannan matsayar tasu za ta shafi sauran zaɓuka da za a gudanar a Kano nan da shekaru masu zuwa? Sai dai ya ce wannan matsayar ta zaɓukan ƙananan hukumomin da za a gudanar a halin yanzu ne kawai, domin a cewarsa, babu wanda ya san gobe.
Shi kuwa Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya ce su a wurinsu, ba PDP ba ce ba za ta shiga zaɓe ba, “Kwankwasiyya ce ba za ta shiga zaɓe ba domin na ji ‘yan PDP sun ce za su shiga zaɓe”.
“Shi wannan wanda yake cewa shi ne shugaban riƙo na PDP, shi ne fa shugaban gudanarwa na Kwankwaso a jihar Neja, mu a wajenmu ba PDP ba ce, Kwankwasiyya ce ke cewa ba za ta shiga zaɓe ba saboda sun san ba za su ci ba,” in ji Abdullahi Abbas.
Ya kuma kare hukumar zaɓen Kano inda ya ce mutane ne masu mutunci kuma masu daraja, a cewarsa, yana ganin za su gudanar da adalci.