Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

An kammala gasar cin kofin kwallon kwando na shugaban hukumar kwallon kwando na kasa Ahmad Musa Kida karo na farko a jihar Kano,

Inda Kungoyar NTM Thunders ta lashe gasar daci 27 da 24 kan Kungiyar Kwallon Kwando ta Ahamadiyya a wasan karshe da aka buga a filin wasan kwallon kwando na jamiar Bayero dake Kano

Da yake Jawabi a Madadin wanda ya dauki nauyin gasar mamba a hukumar kwallon kwando ta kasa Surajo Yusuf yace shirya wasan kwallon kwando a jihar kano wata farar dabarace duba da tasirin da jihar kedashi a kwallon Kwando a fadin tarayyar Najeriya,

Yusif wanda ya bayyana jin dadi da yadda matasa suka taka wasan yace hakan ya tabbatar da irin tarin matasan yan wasa da jihar kedasu da zasu iya zama abin alfahari a fagen was an kwallon kwando ba a kasa Najeriya ba harma da duniya baki daya,

Da yake amsa tambaya kan yadda wasan zai vigaba da gudana Surajo Yusuf cewa yayi shugaban hukumar yace zaa dinga yin wasan duk shekara dan bunkasa wasan daga tushe,

Kan makomar wasan kwallon kwando a Najeriya yusif cewa yayi wasan zai sami bunkasa sakamakon samun masu daukar nauyin wasan da shugaban hukumar Musa Kida yayi na tsawon shekaru biyar inda za a sanya Naira Miliyan 30 kowace shekara abin da yace hakan wani abune da yake nuni da kokarin shugaban na bunkasa wasan a kasa.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *