
An ba da rahoton samun mutane 38 da suka sake kamuwa da annobar cutar kcoronavirus a Najeriya, daga cikin sabbin jihohin da cutar ta bulla karon farko akwai Sokoto da Gombe.
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya ta ce adadin masu fama da cutar ya zuwa 11:10 na daren Litinin sun kai 665.
Sai dai wani labari mai karfafa gwiwa shi ne a Litinin din nan, an samu mutum 18 rigis da suka warke daga cutar a cewar alkaluman NCDC.
Wannan karo jihar Kano ce ta fi samun yawan mutanen da cutar ta sake kamawa da 23, inda adadin masu annobar a Kano ya kai 59.