Daga- Abdullahi Isah
hukumar sadarwa ta kasa NCC ta sanarda rufe layukan wayar salula kimanin miliyan biyu da dubu dari biyu.
Shugaban hukumar ta NCC Farfesa Umar Garba Dambatta ya sanarda hakan a birnin tarayya Abuja.
Farfesa Dambatta yace an rufe layukan ne saboda rashin bin ka’ida wajen yin rajistar layukan.
Ya kuma tabbatar da cewa matakin zaiyi muhimmin tasiri wajen inganta tsaro a Nigeria.