
Ministan lafiya na Najeriya ya yi roko ga masu gine-ginen da babu mutane ciki, da su ba wa gwamnati aro domin mayar da su cibiyoyin killace wadanda ke gida da aka gwada suna da korona.
Dr Osagie Ehanire ya ce za a iya bai wa gwamnatin jihohi gudunmawar gine-ginen da babu kowa ciki don amfani da su na wani dan lokaci.
Bayanin nasa na zuwa ne bayan da daraktan hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta kasar ya ce, jami’ansu na fama da matsalar karancin dagajen da za a aje marasa lafiya a wasu yankuna a kasar.
Ya kara da cewa akwai bukatar mayar da hankali kan jihar Kano da kuma birnin tarayyar Abuja, amma Legas inda nan ce cutar ta fara billa a kasar “ita ce babban kalubalensu”.
Ya ce tawagarsa na duba wasu hanyoyin da za a iya amfani da su ciki har da gidajen raino, amma yanzu haka suna aiki tare da gwamnatocin jijoji domin kawo karshen wannan matsala.