By Abdullahi Isah
Hukumar gudanarwa ta Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta,, ‘Yar Gaya ta bullo da wani sabon tsarin inganta kwazon dalibanta.

Kamar yadda shugabar Makarantar Uwani Ahmad Balarabe, ta bayyana, tsarin ya kunshi bayarda hutun tsakiyar zangon karatu ta yadda dalibai zasu sami hutun kwakwalwa.
Uwani Ahmad tace a yayin makon hutun, daliban zasu gabatar da abubuwan nishadi da muhawara gamida gwajin kwazo domin kara zaburar dasu kan karatunsu.
Wasu daga cikin daliban, sun shaidawa Express Radio cewa sunyi matukar farin ciki da wannan tsarin, kuma hakan zai basu damar dawo da natsuwarsu kafin su koma karatu.
A hannu guda kuma, Umaru Natagunde Gezawa, dake shugabancin riko na kungiyar Iyaye da Malamai na Makarantar, yace duk da yake an Mayard ilmi kyauta, amma a matsayinsu na iyaye, zasu cigaba da bayarda gudunmawa wajen bunkasa ilmi a jihar.