Daga -Abubakar Sale Yakub

Kwamishinan Lafiya ta jihar Kaduna Dr. Amina Muhammad Baloni, ta tabbatar da bullar sabuwar kwayar cutar zazzabin Lassa a jihar.
Tace wani mutum me shekaru 40 aka gano yana dauke da kwayar cutar a ranar Juma’a 21 ga Watan Fabrairu, 2020, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria yana kuma karbar magani a cibiyar da aka tanadarwa wadan da suka kamu da cutar Lassa.
“Wannan shi ya kawo adadin mutane biyu wadan da suka kamu da cutar a jihar Kaduna suna kuma karbar magani a cibiyar da aka ware musu ” a cewar Baloni.