Kamfanoni sun samar da ayyukan yi da yawansu ya kai miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu a watan da ya gabata a Amurka.
Hakan ya sa aka samu raguwar alkaluman rashin aikin yi da ƙasa da kashi goma a karon farko tun bayan ɓullar annobar Korona.
Samun ƙaruwar ayyuka da kuma raguwar rashin ayyukan yi a Amurka watanni huɗu a jere labari ne mai daɗi ga tattalin arzikin ƙasar da ya fuskanci koma baya saboda annobar korona.
To amma har yanzu akwai jan aiki, musamman kan halin da ƙananan kamfanoni suka tsinci kansu tun bayan ɓullar annobar.
Bugu da ƙari an kasa cimma matsaya kan yadda za a ɓullo wa al’amarin a tsakanin Fadar White House da kuma yan majalisa.